Tsohon kocin ya taimaki tawagar Chelsea wajen zama zakarun Ingila tare da daga kofin gasar FA cikin shekara biyu da ya jagorance ta.
Shahararren kungiyar kwallon kafa kuma zakaran kofin FA na kakar bara, Chelsea tayi bankwana da kocinta Antonio Conte bayan shekara biyu da zuwansa.
Labarin sallamar ta fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar kasar Ingila tayi a shafin ta na yanar gizo ranar Alhamis 12 ga watan Yuli.
Haifafen dan kasar Italiya, Antonio Conte ya dawo wajen jagorantar yan wasan kungiyar a kakar 2016.
Tsohon dan wasan mai shekaru 48 ya maye gurbin Mourinho kuma shine koci na 9 da kungiyar tayi cikin tsawon shekaru 15 da Roman Abrahamovic ya zama mammanlakin kungiyar.
Shekarar sa na farko tare da tawagar yayi nasarar lashe kofin zakarun Ingila haka zalika a shekarar sa na biyu yayi nasara daga kofin FA.
Chelsea tayi bankwana da tsohon kocin Juventus bayan shekara biyu duk da kwantiragin sa sai bayan shekara uku zai kare.
Rahotanni sun nuna cewa Kocin kungiyar napoli, Mauricio Sarri, zai maye gurbin sa. Wata kila a kammala yarjejeniyar cinikin kafin karshen makon da muke ciki.
Labarin fitar Conte ya dade yana yawo a kunen wasu da dama bayan labarin rashin jituwa da ake zargin cewa ke faruwa tsakanin sa da wasu yan wasan tawagar.