Ambaliyar Katsina: An gano gawar amarya a Jamhoriyar Nijar

Mutum sama 40 suka rasa rayukan su sakamakon ambaliyar ruwa da ya faru a jihar Katsina

Kamar yadda labari ya bayyana an daura aurenta ga mijinta  Malam Sani Yahaya kwana uku kafin ibtilain ya fado ma al'ummar garin.

An gano gawar wata sabuwar amarya mai suna Hindatu Abubakar a kasar jamhoriyar nijar sakamakon ambaliyar ruwa da ya faru a garin Jibiya na Jihar Katsina.

Kamar yadda labari ya bayyana an daura aurenta ga mijinta Malam Sani Yahaya kwana uku kafin ibtilain ya fado ma al'ummar garin.

Ya sanar ma manema labaran NAN cewa an gano gawar amaryar sa a kauyen Girka dake gundumar Mada-Rumfa nan jamhoriyar Nijar.

Yace bayan bincike da suka wajen gano ta sakamakon ambaliyar ruwar da ya sauka ya samu labari daga garin Girka na Nijar dake makwabtaka da karamar hukumar Jibiya.

Yace anyi sallar jana'izar ta jim kadan bayan karbar gawar ta.

Ruwan sama ya jawo ambaliyar

Akalla mutum sama da 2000 suka rasa muhallin su sakamakon ambaliyar ruwa da ya faru a garin Jibiya dake jihar Katsina.

Kamar yadda hukumomi suka bayyana mummunar ambaliyar yayi sanadiyar mutuwar mutum fiye da 40 kuma gidaje da dama suka lalace sakamakon ruwan saman da aka wayi gari ana yi.

A labarin da BBC ta fitar, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Alhaji Aminu Waziri, ya shaida cewa gidaje fiye da 200 sun rushe kuma tuni aka kai mutane da suka rasa matsugunnan nasu makarantar firamaren da ke garin na Jibiya domin su zauna kafin a samar musu matsugunni.

Post a Comment

Previous Post Next Post