Dan kasuwar wanda ke da shekara 61 a duniya ya dangatanka rashin yin auren sa bayan mutuwar aurensa shekarun baya ga yawan hidindimu da yake da zirga-zirgar kasuwanci.
Jama'a da dama sun bayyana ra'ayoyin su game da kalaman hamshakin mai kudin, Aliko Dangote, dangane da rayuar auren shi.
Hirar shi da jaridar Financial Times, Shugaban kamfanin Dangote yace lokaci yayi da zai nemi abokiyar zama domin shekaru na ta tafiya.
Dan kasuwar wanda ke da shekara 61 a duniya ya dangatanka rashin yin auren sa bayan mutuwar aurensa shekarun baya ga yawan hidindimu da yake da zirga-zirgar kasuwanci.
" Shekaru ba raguwa suke. shekara 60 ba wasa ba. Lamarin ba zaiyi dadi ba idan na nemi wata alhali banda isashen lokaci. A halin yazu dai akwai ayyukla da dama a gaba na",yace.
Kamar yadda ya bayyana, ayyukan dake gaban shi sun hada da gina matatar man fetur da taki da gina sinadarin mai da iskar ta.
Sai dai wasu daga cikin masu sharhi kan lamarin sun ce ba a fahimci ainihin zancen attajirin ba, don a cikin kalaman da ya yi wa jaridar ta FT, bai fito kai tsaye ya ce yana neman matar da zai aura ba.
Wannan ya sa wadansu mata musamman a kafafen sada zumunta suka rika bayyana bukatarsu ta neman auren attajirin, wanda yanzu ba shi da mata.
Ga yadda wasu suka tunkari batun a shafin mu na Instagram:
Hauwa_sarki77 ta rubuta "wallahi i'm in love with him"
Kamal_Muhd_maitafseer "Yaje wajen wata yarinya tace bata sonsa wallahil azeem. Kuma nasanta"
fiddausi_isma_il "waiyo Allah cikina aiyayi tsufa dafama Dan shine"
Ita kuma aisha.lawal.526438 tana tambaya "Wace irin yake nema, budurwa ko tsohuwa, ko madaidai ciya?
A wani bangare kuma wasu suna ma attajirin addua tare da bashi shawara. Ga wasu kamar haka:
Maryanmdabo "Allah ya bashi mata meson Allah Allah ya taimakeshi mata kwarai.
fatima_umar_liman "Allah ya bashi ta gari mai tsoron Allah.
Kai ga yanzu batun ya zama abun muhawara a kafafen watsa labarai dake fadin kasar.
Dangote dai ya samu albarkacin yara mata uku sakamakon auren da yayi shekarun baya.