
An gudanar da sallar a masallacin An-nur dake nan Abuja yammacin ranar alhamis 5 ga watan Yuli.
Dandazon jama'a suka halarcin sallar jana'izar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Marigayi Adamu Ciroma, wanda ya rasu ranar alhamis.
An gudanar da sallar a masallacin An-nur dake nan Abuja yammacin ranar alhamis 5 ga watan Yuli.
Mallam Adamu Ciroma ya rasu ne a wata asibitin kudi dake nan babban birnin tarayya bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Cikin dandazon jama'a da suka halarci jan'izar sa akwai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Sarkin Fika, Mai martaba Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa.
Shima shugaban ma'akatan fadar shugaban kasa, Alhaji Abba Kyari ya halarci jana'izar tare da wasu ma'aikatan fadar shugaban.
Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam tare da takwaran sa na jihar Kebbi Atiku Bagudu suma sun hallara.
Takaitaccen tarihin marigayi
Tsohon jigon jam'iyar PDP ya rasu ranar alhamis 4 ga watan Yuli kuma yana yana da shekaru 84.
Haifafen dan garin Potiskum dake jihar Yobe, shine gwamnan babban banki tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni na 1977.
Bayan haka ya rike matsaayin ministan kudi karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wa'adi na farko na mulkin sa.
Bugu da kari shine shugaban yakin neman zabe na Obasanjo yayin da tsohon shugaban ke neman zarcewa a zaben 2003.
Gabanin rasuwar sa, marigayin ya taka rawar gani a harkar siyasar kasar.