Abdullahi Shehu: Gwamnatin jihar Sokoto ta karrama dan wasan Super Eagles

Abdullahi Shehu yayin da yake motsa jiki gabanin wasan Nijeriya a Rasha

Gwamnan ya baiwa dan kwallon kyautar gida da kujerar hajji da kudi da kuma fili na gina wurin motsa jiki na horas da  matasan jihar.

Fitaccen dan wasan tawagar Super eagles ta Nijeriya, Abdullahi Shehu, ya samu goma ta arziki daga gwamnatin mahaifar shi, Sokto.

Gwamnatin jihar karkashin jagorancin, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta karrama ma shi da wasdu kyaututuka bisa rawar da yake takawa a farfajiyar wasan kwallon kafa.

An shirya taron karramawa ta musamman ga dan wasan bayan Super Eagles a zauren gidan gwamnatin Sokoto ranar litinin 2 ga watan Yuli.

Gwamnan ya baiwa dan kwallon kyautar gida da kujerar hajji da kudi da kuma fili na gina wurin motsa jiki na horas da  matasan jihar.

A jawabin sa wajen taron karramawa, gwamnan yayi kira ga matasan jihar da su kwaikwayi halayen dan wasan. Sun kaurace da zama yan bangar siyasa.

Shima, Abdullahi Shehu, ya baiwa gwamna kyautar rigar tagawar Nijeriya mai dauke da sarautar jagoran jihar sokoto "Matawalle".

 

Bugu da kari dan wasan ya nuna farin cikin sa bisa karamcin da gwamnatin tayi masa. A sakon da ya wallafa a shafin sa na kafafen sada zumunta, dan wasan ya lissafa kyautar da ya samu tare da yi gwamnatin godiya.

Yace abun godiya ne zama jakadan jihar sa kuma zaiyi iya bakin kokarin sa wajen taimakwa al'ummar jihar.

Abdullahi Shehu, yana daya daga cikin yan wasan Nijeriya da suka nuna bajinta a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Duk da cewa Super eagles bata yi nasara fita daga rukunin ta ba domin kaiwa zagaye na biyu a gasar wanda ke ci har yanzu, yan wasan tawagar sun samu yabo da jinjina bisa rawar da suka taka.

Post a Comment

Previous Post Next Post