
Ganduje yace maganar Kwankwaso na nuna cewa ya zama rudadden dan siyasa wanda ke kama duk wata dama da ta zo masa domin ya dawo da matsayinsa a siyasance.
Bayan furucin da tsohon gwamnan jihar Kano yayi dangane da zaben nan gaba, gwamnan jihar na yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar masa da martani na cewa ko a mazabar shi samun nasara zai gagare shi.
Yayin da ya zanta da fitaccen dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation wato Dele Momodu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa a halin yanzu bai da jam'iya amma idan PDP ta bashi dama zai kada shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Yana mai cewa "PDP na bukatar dan takara wanda ya fito daga jihar Kano ko Kaduna ko kuma Katsina idan har tana son ta yi nasara a zaben takarar shugaban kasa domin sune jihohin da suka fi samun yawan kuri'u".
Ya kara da cewa shine ya cancanci fitowa takara karkashin jam'iyar.
Martanin da Ganduje ya mayar wa Kwankwaso
Dangane da ikirarin da yayi, gwamnan Kano kuma tsohon mataimakin sa, Abdullahi Umar Ganduje, yace ko a mazabar da yake yin zabe, kwankwaso ba zai iya lashe kuri'u ba balle ya kayar da Buhari.
Gwamnan ya fadi hakan ne a wata takardar sanarwa da kwamishnan yada labarai na jihar Kano, Muhammed Garba, ya sanya wa hannu.
Ganduje yana mai cewa "Maganar Kwankwaso na nuna cewa ya zama rudadden dan siyasa wanda ke kama duk wata dama da ta zo masa domin ya dawo da matsayinsa a siyasance.
"Sama da shekara uku yana Majalisar dattawa yana barci ba tare da ya gabatar da kudurin da zai amfani mutanen Najeriya ba,".
Gwamnan dai ya kara da cewa tun sama da shekaru uku da yake majalisar dattawa bai ziyarci mazabar shi ba kuma bai gudanar da wani aikin azo a gani ba.
Sauyawa zuwa jam'iyar PDP
Har yanzu dai Kwankwaso bai fito fili ya bayyana cewa ko ya bar jam'iyar APC duk da cewa alamu na cewa ya sauya sheka zuwa tsohon jam'iyar shi ta PDP.
Wasu masana harkokin siyasa suna ganin cewa tuni tsohon gwamna ya riga ya sauya sheka duna da take-taken da yake yi kwana-kwanan nan.
A makonin da suka shude, Sanatan ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yayin da APC ke gudanar da babban taron ta. Hakazalika ya kuma ziyarci gwamna Ayo Fayose kuma ya bayyana goyon bayan sa ga dan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin PDP a zabe wanda za'a gudanar nan bada dadewa ba.
Idan har Kwankwaso ya fice daga APC zuwa PDP, zai shiga sahun manyan ya'yan jam'iyar dake neman kujerar shugaban kasa.
A halin yanzu Ahmed Makarfi, Ayo Fayose, Datti Baba-Ahmed, Atiku Abubakar, Kabiru Tanimu Turaki, Sule Lamido da Mallam Ibrahim Shekarau suka bayyana anniyar su na tsayawa takara a karkashin jam'iyar PDP.