Shugaban rundunar ta Karnataka State Reserve Police ya shaida cewa ya damu da yadda matsalar kiba ke kara yawa tsakanin jami'an rundunar.
Rundunar yan sanda ta kasar Indiya ta gargadi wasu jam'an ta da su yi gaggawa wajen rage kiba ko kuma a sallame su daga aiki.
Shugaban rundunar ta Karnataka State Reserve Police ya shaida cewa ya damu da yadda matsalar kiba ke kara yawa tsakanin jami'an rundunar.
Kamar yadda BBc ta ruwaito shugaban, Bhaskar Rao, yace an dau wannan matakin ne bayan da aka samu jami'an rundunar su 100 da suka rasu sakamakon matsalar kibar jiki.
Sai dai yayi kira ga sauran al'umma da su taimaki jami'an da hanyoyi da zasu taimaka wajen kula da lafiyarsu.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an rundunar yan sanda ta gundumar Karnataka su na samun yawan kira domin kwantar da tarzoma alhali jami'am ta sun kai 14,000.
Bugu da kari an kuma gane cewa jami'an suna yawan cin abinci musamman shinkafa da soyayyen abinci wadanda ke haddasa matsalar kiba da suke fuskanta.