A jihar Kano: Maryam Abacha zata hada gwiwa da gwamnatin Kano domin kawo karshen ta'amali da miyagun kwayoyi

Hajiya Maryam Abacha

Hajiya Maryam ta bayyana haka ne yayin da take kaddamar da sabuwar gudauniyar Sani and Maryam Abacha Support Foundation a jihar Kano.

Matar tsohon shugaban kasa Maryam Abacha ta sha alwashin hada gwiwa da gwamnatin jihar Kano wajen kawo karshen yawan amfani da miyagun kwayoyi.

Hajiya Maryam ta bayyana haka ne yayin da take kaddamar da sabuwar gudauniyar 'Sani and Maryam Abacha Support Foundation' a jihar Kano daren ranar asabar 28 ga wata.

Tace yin haka ya zama dole domin karafafa gwiwar gwamnatin wajen kawo karshen abun takaici dake haihafa tsakanin matasa a al'umma.

Ta kara da cewa matakin gina wannan gidaubiyar ta faru ne bisa ga kokarin da ita da sauran iyalen ta suke yi wajen taimakawa al'umma.

Matar marigayi Sani Abacha tace gidauniyar zata kuma hada kai da masarautar Kano domin wayar da kan al'umma a bangarin dogaro da kai da bunkasa harkar ilimin zamani da na addini tare da wayar da kan al'umma wajen hakan amfani da miyagun kwayoyi dake halaka rayuwar matasa da matan aure.

A jawabin sa wajen taron kaddamarwa, babban danta kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano Alhaji Muhammed Abacha yace makasudin kafa wannan gidauniyar shine domin bunkasa zaman lafiya tare da samada da walwala da bunkasa kasuwanci a cikin al'umma.

Yace gidauniyar zata mayar da hankalin ta a bangaren matsalar rashin ilimi, talauci, miyagun kwayoyi da makamantar matsaloli dake ci ma al'ummar arewa tuwa a kwarya.

Post a Comment

Previous Post Next Post