Ziyara aiki: Yadda shugaba Buhari ya samu tarba a kasar Morocco

Kamar yadda sanarwar da kakakin shugaban Garba Shehu ya bayyana, shugaban ya tafi kasar ne bisa gayyatar da sarkin Morocco ya tura masa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Morocco yammacin ranar lahadi 10 ga watan Yuni.

Ya samu kyakyawar tarba daga sarkin Morocco yayin da ya sauka birnin babban birnin kasar. Bayan ga haka mai alfarma sarkin Morocco Muhammed na shidda ya shirya masa biki na yi masa mara ba da zuwa a fadar sa.

 

Kamar yadda sanarwar da kakakin shugaban Garba Shehu ya bayyana, shugaban ya tafi kasar ne bisa gayyatar da sarkin Morocco ya tura masa.

 

Zasu tattauna ne kan hanyoyin inganta harkar kasuwanci tsakakin kasashen.Wannan ya biyo bayan ziyarar da sarkin ya kawo Nijeriya cikin shekarar 2016.

 

Muhimman batutuwa da zasu tattauna a kai sun hada da samun matsaya kan yarjejjeniyar inganta masana'antar takin zamani. Hakalizaka zasu tattauna kan samad da ingantaccen tsarin ilimi da hanyoyin tsarrafa iskan gas da sauran ma'adanai kimiya.

Shugaban dai ya ziyarci kasar tare da gwamnan jihar Ebonyi David Umahi da takwaransa na jihar Jigawa Alhaji Abubakar Badaru tare da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post