Yayin da take amsa tambayoyi wanda ake zargi da siyan jaririyar ta shaida cewa ta siya diyar ne kan naira N360,000.
Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama wata mahaifiya mai suna Blessing Chukwu kan laifin siyar da jariyar ta wanda ta haifa mako uku baya.
Kamar yadda rahoto ya bayyana an kama ta tare da wadanda suka yi cinikin siyar jaririyar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan sanda sun kuma kama wani likita Kelechi da matarsa Puphemia kan zargin taimakawa wajen gudanar da cinikin a asibitin su dake nan garin Okigwe dai dai inda aka haifi jaririyar.
Yayin da take amsa tambayoyi misis Okpara wanda ake zargi da siyan jaririyar ta shaida cewa ta siya diyar ne kan naira N360,000.
Tace ta yanke shawarar yin hakan ne bayan shafe tsawon shekaru 13 da yin aure bata samun albarkar da ko diya ba.
A nata bayanin, mahaifiyar wanda ake zargi ta sanar cewa an biya ta N190,000 bayan ta siyar da jaririyar wacce take na biyar daga cikin yaran da ta haifa duk ba tare da yin aure ba.
Mahaifiyar mai shekaru 22 tace tayi hakan ne domin samun kudin kulawa da sauran yaran ta.
Kamar yadda Punch ta ruwaito an kama dukannin su ne a daidai asibitin tarayya dake nan Umuahia inda jaririyar take karban kulawa sati uku bayan haihuwar ta.