Za'a daura auren shi ga amarya, Fatima Ibrahim, ranar 30 ga watan Yuni a nan garin Kano.
Fitaccen jarumin fina-finan hausa, Ramadan Booth, ya dau damara inda ana kirga yan kwanaki kafin a daura auren shi.
Za'a daura auren shi ga amarya, Fatima Ibrahim, ranar 30 ga watan Yuni a nan garin Kano.
Jarumin ya daura hotunan kafin aure da suke yi a shafin sa na Instagram. A halin yanzu hatunan su ya mamaye duniyar gizo inda sauran abokan aikin sa a masana'antar kannywood da masoyan sa suke daurawa a shafukan su tare da yi masu fatan alheri.
Kamar yadda muka samu labari an shirya wasan motsa jiki na musamman domin raya auren su.
An kasa yan wasan kwallo kuma Ali Nuhu zai jagoranci bangare guda kana Adam Zango zai jagoranci dayan tawagar.
Wasan kwallon "Amarya da ango" zai samu halarcin manyan fuskoki na masana'antar fim tare da sauran abokan sa.
Dangane da auren, jaruma Maryam Booth, wacce take yar'uwa a gareshi, ta bayyana cewa a gidan sa zata dinga tare wa domin cin abinci. Ta fadi hakan ne a bangaren tsokaci bayan saka hotunan kafin aure da yayi.