Shugaban kasa Muhammmadu Buhari ya shirya liyafar bude baki ma wasu kungiyoyin matsa da fitattun jaruman dandalin nishadantarwa na kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakonci wasu kungiyoyin matasa da fitattun jaruman dandalin nishadi a fadar sa.
Matasan da jaruman sun yi bude baki tare da shugaban a fadar sa yammacin ranar alhamis 7 ga watan Yuni.
Shugaban ya shirya liyafan ne don karrama matasan maza da mata bisa gudummawar da suke baiwa kasar ta hanyar aikin da suke.
Jami'an gwamnati da suka halarci wajen taron tare da shugaban sun hada da shugaban ma'aikatan fadar shugaban Mallam Abba Kyari da shugaban hukumar samad da wutan lantarki dakta Sanusi Ohiare.
Yan wasan sun hada da na masana'antar kudancin kasa da na Kannywood tare da wasu shahararrun mawaka da ake damawa dasu a kasar.
Manyan yan wasan da suka halarci taron sun hada da Sound Sultan da Small Doctor da shaharren mai shirya fim Kunle Afolayan tare da Adebayo Salami.
Jaruman Kannywood da suka halarcin liyafar sun hada da Mawaki Ali Jita, Nazifi Asnanic da Dauda Kahutu Rarara.
A bangaren jarumai kuwa akwai Yakubu Muhammed da Ibrahim Maishunku da Uzee Usman da Adam A.Zango da Baban cinedu da wasu masu hannu da shuni na masana'antar fim.
Wannan na daga cikin jerin liyafar bude baki da shugaban ya shirya tare da wasu yan kasa cikin watan Ramadan na bana.