Shugaban yace gobarar yana daga cikin hadura mafi muni da ya faru a kasar kwana-kwanan nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna takaicin sa kan mummunar gobarar da ya faru a babban titin jihar Legas.
Sama da motoci 50 suka kama da wuta a lokacin da motar makare da mai ta kufce, sannan man da take dauke da shi ya malale a kan titi.
Mummunar gobarar ya faru ne yammacin ranar alhamis yayin jama'a ke zirga-zirga bayan da burkin motar ya katsare a daidai gadar Otedola dake nan jihar Legas.
A sakon da ya fitar, shugaban ya nuna nuna bakin cikin sa sakamakon gobarar da ya haifar da asarar dukiyoyi da rayuka.
"Abun takaici, wannan ya zamanto daya daga cikin hadura mafi muni da ya faru a kasar kwana-kwanan nan"shugaban yace.
Shugaban yayi ma gwamnatin jihar tare da al'ummar ta jaje tare da yin kira ga ma'aikata da jami'an hukumar agaji da su yi iya bakin kokarin su wajen rage radadin da gobarar ya haifar.
Daren ranar da gobara ya faru shima gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya kai ziyara dai-dai titin da mummunar lamarin ya faru domin ganin illar da gobarar ya haifar tare da taya al'ummar da gobarar ta ratsa jaje.