Mummunar gobarar ya faru ne yammacin ranar alhamis yayin da a da burkin motar ya katsare a daidai gadar Otedola dake nan jihar Legas.
Sama da motoci 50 suka kama da wuta a lokacin da motar makare da mai ta kufce, sannan man da take dauke da shi ya malale a kan titi.
Mummunar gobarar ya faru ne yammacin ranar alhamis yayin da a da burkin motar ya katsare a daidai gadar Otedola dake nan jihar Legas.
Jami'an ma'akatar agaji na gaggawa ta jihar sunyi iya bakin kokarin su wajen kashe gobara da faru.
Kamar yadda shaidu suka bayyana, ba'a kayyade adadin mutane da gobarar yayi sanadin ajalin su amma anyi asara da dama.
Lamarin dai yayi jawo bakin ciki a zukatan yan kasa inda a fadin kasar a halin yanzu ana cigaba da nuna takaicin ta tare da yin kira ga jami'an gwamnati wajen samad da hanyar rage mummunar asara dake faruwa a kasar.
Tags:
News