Yan wasa Ahmed Musa da Shehu Abdullahi tare da sauran ma'aikatan tawagar sun raya wannan ranar tare da yima daukacin musulmai fatan alheri.
Al'ummar musumai a kasashen duniya sun waye gari da farin cikin karamar sallah bayan kammala azu in watan Ramadan.
A kasar Rasha kuwa inda idon duniya yake a halin yanzu kasancewa nan ake gudanar da gasar cin kofin duniya, suma yan wasan Nijeriya sun gudanar da idi.
Wasu yan tawagar Super eagles sun gudanar da sallar idi tare da sauran al'ummar kasar Rasha gabanin wasan su na farko da Croata a gasar wanda zasu buga ranar asabar 16 ga watan Yuni.
Yan wasa Ahmed Musa da Shehu Abdullahi tare da sauran ma'aikatan tawagar sun raya wannan ranar tare da yima daukacin musulmai fatan alheri.
A wata sakon bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Instagram, dan wasan bayan Nijeriya kuma dan asalin jihar Sakwato, Shehu, yayi musulmai murna zagoyowar wannan ranar farin ciki.
Jama'ar nijeriya dai sun sa ido tare da yima tawagar yan wasan fatan alheri a gasar wanda aka fara ranar alhamis 14 ga wata.
Nijeriya tana rukuni daya da kasar Argentina da Croatia da Iceland.