
A wasan wanda aka tashi 2-0 dan wasan kungiyar Leicester na Ingila, Ahmed Musa, ya saka kwallo farko a raga cikin minti 49 kana ya kara a cikin minti 75.
Tawagar yan wasan super eagles na Nijeriya basu yio sakaci ba wajen faranta wa al'ummar kasa rai ba wasan su da kasar Iceland.
Wasan ta na biyu a gasar cin kofin duniya, Nijeriya ta doke kasar nahiyar turai da 2-0.
Dan wasan gaba, Ahmed Musa, ya daga tutar kasar inda ya taimaka wajen zurra kwallaye biyu a ragar Iceland. Gabanin wasan Nijeriya bata maki ko daya sakamakon rashin nasara da tayi wasan ta na farko da kasar Croatia duk a rukunin D na gasar.
Dan wasan kungiyar Leicester dake kasar Ingila ya saka kwallo farko a raga cikin minti 49 kana ya kara a cikin minti 75.
Da wannan nasarar, tawagar ta samu maki uku kuma idan har ta samu maki daya wasan ta na karshe da Argentina Nijeriya zata tsallake zuwa zagaye na biyu.
Nasarar dai ya jawo abun alfahari a fadin kasar har ma da kasashen waje inda yan Nijeriya da sauran kasashe ke jinina ma tawagar bisa bajinta da suka nuna a wasan yau.