Gasar cin kofin duniya: Argentina ta katse gudun tawagar super eagles a gasar wannan shekara

Super Eagles were praised after Lionel Messi inspired Argentina to a 2-1 victory in their final group D game of the 2018 FIFA World Cup, on Tuesday, June 26

Daf da lokacin tashi, dan wasan baya, Marcos Rojo, ya lallata lissafin wasa ma tawagar Super Eagles.

Ba'a so haka ba, Argentina ta katse gudun tawagar super eagles a gasar kofin duniya wasan su na karshe a rukuni.

Wasan wanda aka buga daren ranar talata 26 ga watan Yuni, Argentina tayi nasara da ci biyu da daya (2-1).

Jagoran yan wasan kasar nahiyar kudancin Amurka, Lionel Messi, ya fara zura kwallo a ragar mai tsaron gidan Nijeriya. Bayan dawowa hutun rabin lokaci, Victor Moses, ya rama sakamakon fenerti da Nijeriya ta samu.

 

Daf da lokacin tashi, dan wasan baya, Marcos Rojo, ya lallata lissafin wasa ma tawagar Super Eagles.

Wasan dai zata taimaki Nijeriya wajen tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar idan aka tashi kunnen doki ko Nijeriya tayi nasar. Sai dan wasan kungiyar Manchester United ya hana Nijeriya cinma wannan matakin cikin minti 85 na wasan.

 

Lamarin dai bai yi ma tawagar dadi amma jama'a da dama sun yaba gogewa da jajircewa da yan wasan suka yi a gasar bana.

Har yanzu dai sakamakon wasan ya zama batun muhawara a kafafen watsa labarai da kafafen sada zumunta.

Hakika sakamakon wasan bai yi ma jama'ar Nijeriya dadi ba kuma da hakan Nijeriya zata shiga sahun sauran kasashen Afirka uku da suka riga su rashin nasara wajen tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Yanzu dai arkalla ta koma ga kasar Senegal wanda ita kadai ta rage daga nahiyar Afrika. Wasan su na karshe na rukuni da kasar Kolonbiya zai tabbatar da matsayin su a gasar bana.

Post a Comment

Previous Post Next Post