A hoton da yake yawo a kafafen sada zumunta za'a gan inda matar mataimakin shugaban kasa take daura ma Aisha Buhari dankwali
Hoton matar shugaban kasa Aisha Buhari tare da matar mataimakin shugaban ya jawo hankalin jama'a a kafafen sada zumunta.
A cikin hoton wanda hadimin shugaban kasa ya wallafa a shafin sa na kafar sadarwa, za'a gan inda Matar mataimakin shugaba kasa Dolapo Osinbajo take ma uwargidan shugaban daurin dankwali.
Hoton dai ya jawo hankalin jama'a a duniyar gizo inda wasu ke ganin cewa sun birge sosai kasancewa uwargidan shugaban kasa tana da damar sa yar aikin fada yin aikin da matar mataimakin shugaban kasa tayi.
Tags:
News