Kasar dake makwabtaka da Nijeriya ta fara azumin ta ne kwana daya kafin a sarkin musulmi ya sanar da ganin watan ramadan.
Yayin da ya yan Nijeriya ke kyautata zato kammala azumin watan Ramada bayan faduwar rana, a kasar Jamhoriyar Nijar yau ake bikin karamar sallah.
Kasar dake makwabtaka da Nijeriya ta fara azumin ta ne kwana daya kafin a sarkin musulmi ya sanar da ganin watan ramadan.
Firai ministan Nijar, Birji Rafini ya sanar da ganin watan Shawwal ranar Laraba inda yau alhamis al'ummar kasar suka waye gari da murnar ragoyowar karamar sallah.
A ko wace shekara batun ranar fara azumin watan Ramadan yakan jawo cece-kuce a kasashen duniya inda da dama ranar farawa yakan sha bamban.
A rahoton da BBC ta fitar, wasu daga ciklin yan kasar sun nuna farin cikin su kammala azumi sai dai kuma wasu sun koka cewa sallar tazo ba dadi.
Sun danganta haka ga rashin tattalin arziki tare da zafin rana da suka fuskanta yayin azumi.