Ministan yace wannan mataki ne da gwamnatin yanzu take yi na karrama wadanda suka taimaka wajen daga martabar kasar.
Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da aka dauka na baiwa tsohon kociyar tawagar Super eagles gida bisa ga taimakkon da ya baiwa tawagar na lashe kofi a 1994.
Tsohon kociyar Bonfere Johannes ya jagoranci yan wasan Nijeriya wajen lashe kofin zakarun Afrika a cikin shekarar 1994 da gasar olympic na 1996.
Bayan yin nasarar lashe kofin a 1994 gwamnatin wancan lokaci tayi masa alkawarin mika masa gida bisa rawar da ya taka. Gwamnatin mulkin soja na tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ta dau wannan alkawarin.
Ministan muhalli Babatunde Fashola ya mika masa makulli gida mai daki uku a garin Abuja ranar 6 ga watan Yuni.
Ministan yace wannan mataki ne da gwamnatin yanzu take yi na karrama wadanda suka taimaka wajen daga martabar kasar.
Yayin da ya kaddamar da makullen gidan ga tsohon kocin, Fashola yayi masa godiya bisa jajircewan da yayi a shekarun baya da tawagar yan wasan Nijeriya.
Yace an samu jinkiri ne bisa wasu abubuwa da suka shawo kan gwamnati wanda daga baya sun warware su.
A nashi jawabin Johannes Bonfere ya nuna farin cikin sa ga gwamantin tarayya na cika alkawarin da aka dauka tsawon shekaru 24 baya.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta cigaba da tallafawa shirye-shiryen hukumar wassanin motsa jiki domin inganta harkar a kasar.
Daga karshe yayi ma tawagar Nijeriya fatan alheri a gasar cin kofin duniya wanda zai gudanan a kasar Rasha.
Gidan da aka mika masa yana nan a cikin jerin gidaje dake nan Gwagwalada na garin Abuja.