Bikin sallah: Kalli kayatattun hotunan hawan Nasarawa na Kano

Hotunan hawan Nasarawa na bana

Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi Na biyu, ya jagoranci sauran al'umma wajen zagayen hawan Nasarawa ranar lahadi

Duk a cikin bukukuwan murnar zagoyowar karamar sallah, al'umar garin Kano sun gudanar da hawan Nasarawa kamar ta saba yi ko wacce shekara.

Sarkin kano, Mai martaba Muhammad Sanusi na biyu, ya jagoranci masu zagayen wajen raya wannan rana ta uku na bikin karamar sallah.

 

Al'ummar garin Kano sun fito a dandazon su domin kallon masu zagayen ranar lahadi 17 ga wata.

 

Hawan nasarawa ya biyo bayan kwana daya da gudanar da hawan Daushe wanda aka yi a garin.

Abun birgewa na wannan hawan shine yadda sarki tare da sauran jama'a masu agayen suke ado mai birgewa tare da yi ma doki kwalliya.

 

Kamar yadda aka saba, sarkin kano tare da mabiyan sa suna kai ziyara ne ga gwamnan jihar domin taya shi murnar.

 

Hawan dai ya jawo mutane da dama yan kallo ciki har da wasu daga sauran jihohin Nijeriya har ma da kasar waje.

Post a Comment

Previous Post Next Post