Abdulrahman Jimeta: Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Adamawa ya rasu a kasar Saudiya

Adamawa Governor's Chief of Staff, Jimeta, dies on Hajj trip

Ya rasu a safiyar ranar litinin 18 ga watan Yuni yayin da yake aikin umra

An samu labarin mutuwar Alhaji Abdulrahman Jimeta, shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Adamawa wanda ya rasu a kasar Saudiya yayin aikin Umra.

Labarin mutuwar sa ya fito ne a wata sanarwa da kwamishnan labarai, Ahmad Sajoh, ya fitar. Kamar yadda ya sanar, marigayin ya rasu ne a safiyar ranar litinin 18 ga watan Yuni.

Gwamnan jihar Adamawa, Jibrila Bindow, ya yabin halayan sa da kuma jajircewan da yayi wajen samad da cigaba a jihar.

An jana'izar shi a kasar Saudiya bisa ga yardar iyalen sa.

Ya rasu yana da shekaru 59 kuma ya bar mata daya da yara 11.

Post a Comment

Previous Post Next Post