A jihar Borno: Akalla mutum 31 suka rasu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai washe garin sallah

Chibok schoolgirl, Dorcas Yakubu, turns 20 in Boko Haram custody

Bayan harin da suka kai, yan ta'addar sun kuma bude wuta ga taron jama'a dake murnar bikin sallah  a garin Damboa tare da harba gurneti.

Wasu yan ta'ada da ake kyuattata zaton cewa mayakan boko haram sun kai harin kunar bakin wake garin Damboa dake jihar Borno washe garin ranar sallah.

Harin wanda suka kai  daren ranar asabar 16 ga watan Yuni yayi sanadiyar mutuwar mutune da dama.

Sai rahotannin sun sha banbam game da adadin mutane da suka rasu. Hukumar kai agaji ta NEMA tace akalla mutum 20 suka rasu.

A wasu rahotanni kuma sun ce mutum 31 suka rasu yayin da mutane da dama suka jikkata.

Kamar yadda rahotanni  suka ruwaito yan kuna bakin wake shidda, dukkanin su mata, suka kai harin.

Bayan harin da suka kai, yan ta'addar sun kuma bude wuta ga taron jama'a dake murnar bikin sallah  a garin Damboa tare da harba gurneti.

Daya daga cikin yan kato da gora dake garin ya shaida wa yan jarida cewa mutum 31 suka rasu kuma adadin na iya karuwa saboda wadanda suka samu rauni wanda ake iya cewa rai yana baki.

Hukumar NEMA tace an tura jirage masu saukan angulu garin domin daukar wadanda harin ya shafa zuwa Maiduguri.

Post a Comment

Previous Post Next Post