A garin Minna: Yan bindiga sun far ma gidan yari, wasu da dama sun kubuta

4 killed, 7 recaptured as 36 prisoners escape from prison

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kula da lamuran gidan yari, Rabiu Shuaibu ya bayyana, an kashe wani jami'in hukumar sanadiyar arangamar da ya faru tsakanin yan bindiga da jami'an tsaro.

Abun takaici ya faru a garin minna  inda wasu yan bindiga suka far ma gidan kaso dake nan garin tare taimakawa wasu wajen kubuta daga gidan.

Lamarin ya faru a daren ranar lahadi a gidan yarin dake nan unguwar Tunga.

Wannan  yana daya daga cikin ire-iren harin kubutar da wadanda aka tsare a gidan yari da zai faru kwana-kwanan nan.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kula da lamuran gidan yari, Rabiu Shuaibu ya bayyana, an kashe wani jami'in hukumar sanadiyar arangamar da ya faru tsakanin yan bindiga da jami'an tsaro.

Ban jami'in hukumar, yan bindigar sun halaka wani mai babur wanda ke safarar ma'aikacin gidan yari.

Sai dai ba'a san adadin wadanda suka yi nasarar kubuta daga gidan kaso amma an kama wasu daga ciki su bakwai.

Rabiu Shuaibu ya kara da cewa hukumar zata yi iya bakin kokarin ta wajen kama wadanda suka gudu daga gidan kason.

Yayi kira ga sauran jama'a jihar da ma kasar da su taimakawa hukumar wajenn kama wadanda suka kubuta.

Post a Comment

Previous Post Next Post