Ziyarar Super eagles zuwa villa: Buhari yayi kira ga yan wasan Super eagles gabanin gasar cin kofin duniya

Shugaban kasa ya gana da yan wasan super eagles

A jawabin sa yayin da suka ziyarci fadar shi ranar laraba 30 ga watan Mayu, shugaba Buhari yayi kira ga yan wasan da su kasance abun koyi kasancewar su na zama yan wasa mafi karancin shekaru da zasu kara a gasar kofin duniya a tarihin Nijeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakoncin yan wasan kwallon Nijeriya inda ya ja kunnen su gabanin karawar su a gasar cin kofin duniya.

Yan wasan Super eagles tare da wasu jami'an hukumar kwallon kafan Nijeriya ta NFF sun kai masa ziyara ne don neman yardar sa kafin su zarce gasar.

 

A jawabin sa yayin da suka ziyarci fadar shi ranar laraba 30 ga watan Mayu, shugaba Buhari yayi kira ga yan wasan da su kasance abun koyi kasancewar su na zama yan wasa mafi karancin shekaru da zasu kara a gasar kofin duniya a tarihin Nijeriya.

Shugaban ya gargade su da su sani cewa zuwan su Rasha, suna masu daukaka tutar kasar tare da jagorantar dinbim jama'ar kasa.

Yayi kira da su kasance masu kwatanta adalci yayin buga wasanni ba tare da nuna wariya ko kyamar wadanda zasu fuskanta.

 

A jawabin sa, mai horas da yan wasan Nijeriya, Gernot Rohr ya shaida ma shugaban cewa zasu iya bakin kokarin su wajen daga martaban Nijeriya a gasar.

Shima jagoran yan wasan, Mikel Obi ya jaddada magana sa inda ya kara da cewa zasu yi kokarin cin kofin.

Mikel ya kuma bayyana cewa zasu jajirce a gasar kasancewa a wannan karo hukumar kwallo ta biya su dukanin alwus da ya kamace su kafin su zarce zuwa gasar. Yace wannan matakin zai kara baiwa yan wasan karfin gwiwa wajen buga wasa tare da kare martaban Nijeriya.

Bayan ziyaran da su kai fadar shugaban, yan wasan sun zarce zuwa birnin London inda zasu kara da kasar Ingila da Czech Republic a wasanin sada zumunci gabanin gasar kofin duniya wanda zata fara ranar 14 ga watan Yuni.

Nijeriya tana rukuni daya da kasar Argentina da Iceland da kuma Croatia.

Yan Nijeriya sun mika tutar kasar ga tawagar domin su daga ta ga idon duniya a gasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post