Rev Jolly Nyame: Tsohon gwamna zaiyi shekaru 28 a gidan yari kan laifin wawure kudin jama'a

Court sentences ex-Taraba Governor, Jolly Nyame, to 14 years imprisonment

Ya samu hukuncin ne a zaman kotu da aka yi ranar laraba 30 ga watan Mayu bayan karar da hukumar dake hana masu yi ma tattalin arzikin zagon kasa ta EFCC ta shigar a kansa.

Babban kotun tarayya dake garin Abuja ta yanke ma tsohon gwamnan jihar Taraba, Rebren Jolly Nyame hukucin zama a gidan yari na tsawon shekaru 28.

Tsohon gwamnan ya fuskancin wannan hukuncin bayan an kama shi da laifin wawure kudin jihar na naira biliyan N1.64.

Ya samu hukuncin ne a zaman kotu da aka yi ranar laraba 30 ga watan Mayu bayan karar da hukumar dake hana masu yi ma tattalin arzikin zagon kasa ta EFCC ta shigar a kansa.

Hukumar ta shigar da kararraki da dama akan sa wadanda suka shafi laifin rashawa tun a cikin shekarar 2007 wanda daga bisani aka fara sauraro cikin 2010.

A zaman da aka yi, mai shari'a Adebukola Banjoko ya yanke masa hukunci inda ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya sabawa yardar da jama'ar jihar suka lika masa a matsayin shugaba kana ya yanke masa hukuncin ne bayan  kaddamar da wasu shaidu wadanda suka ytabbatar da laifin sa.

A cikin watan Yuli na 2017 aka kara sauraron karar sa a kotun tarayya wanda daga bisani sai yanzu aka zantar masa da hukunci.

Game da Jolly Nyame

Rebren Jolly Nyame ya rike mukamin gwamnan jihar Taraba tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 karkashin jam'iyar PDP. Gabanin 1999, ya rike kujerar mulkan jihar tsakanin 1992 zuwa 1993.

Haifafen karamar hukumar Zing na jihar, Jolly Nyame ya sauka daga kujerar gwamna bayan wa'adin sa ya kare inda Tsohon gwamna Danbaba Suntaio ya maye gurbin sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post