Dan wasan mai tauraro ya bayyana a shafin sa na Tuwita cewa yana murmurewa kuma za'a gan shi a gasar world cup wanda zai fara a cikin watan gobe.
Zakaran firimiya na bana kuma dan wasan kungiyar Liverpool, Mohamed Salah ya bada tabbacin cewa zai samu damar taka leda ma Kasar sa a gasar cin kofin duniya.
Tsabanin jita-jitan dake yaduwa cewa ba zai samu damar yin haka sakamakon karayar da ya samu wasan su da Real Madrid a gasar gane zakarun turai.
Bayan wasan, mai horas da kungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana ma manema labarai cewa dan wasan ya saumu rauni mai tsoratarwa.
Ana sa ran cewa ba zai samu damar taka leda a gasar duniya bayan yayi nasarar taimakon kasar sa wajen shigar ta.
Dan wasan mai tauraro ya bayyana a shafin sa na Tuwita cewa yana murmurewa kuma za'a gan shi a gasar world cup wanda zai fara a cikin watan gobe.
Ya kara da dayi ma dinbim masoyan yan sa godiya bisa fatan alheri da suke masa gabanin raunin da ya samu.
Wasan su na karshe na gasar Champions league, Salah ya fita a fili cike da hawaye sakamakon ketar da dan wasan bayan Madrid, Sergio Ramos yayi masa wanda yayi sanadiyar sa na samun karaya a kafadar sa.
Fitar daga wasan bayan minti 25 da farawa ya razana sauran yan wasan kungiyar Liverpool wanda daga bisani Real Madrid ta doke su da ci 3-1.
Jama'a da dama masu bibiyan lamuran kwallon kafa da masoyan dan wasan sun nuna facin ran su game da ketar da ya auku gareshi.
Lamarin ya zama abun muhawara a kafafen sada zumunta da makamantar gidajen watsa labarai. kamar yadda muka samu labari yan kasar Masar basu ji da dadi ba game da raunin da ya samu kana suna masu yi ma dan wasan Madrid mummunar fata tare da kiran sa da munanan suna.
Duk da cewa shima dan wasan Madrid, Dani Carvajal bai samu ya kammala wasan ba sakamakon raunin da ya samu, jama'a basu yi la'akari da lamarin shi ba.
Bayan wasan dai, Sergio Ramos ya mika sakon fatan alheri na samun sauki ga Mohamed Salah.
Dan wasan yayi hakan ne a ta hanyar shafin sa na tuwita tare da jaddada cewa kwallon kafa ta gaji hakan.