Za'a yi wasan sada zumunci ne a filin wasa na Adokiye Amiesimaka Stadium dake garin Port Harcourt.
Tawagar super eagles ta Nijeriya na shirin karawa da yan wasan kasar DR Congo yau litinin 28 ga wata.
Za'a yi wasan sada zumunci ne a filin wasa na Adokiye Amiesimaka Stadium dake garin Port Harcourt.
Wasan yana daga cikin wasanin da Super eagles zata yi da wasu kasashe kafin gasar cin kofin duniya wanda za'a fara a watan gobe.
Yau shine karo na tara da kasashen zasu hadu. Cikin haduwa takwas da suka yi, Nijeriya tayi nasara har sau biyar yayin da ita Congo tayi nasara lashe wasa uku.
Ana kyautata zaton cewa yan Nijeriya zasu nuna gwanintar su a wasan domin biyan fansar wasar su da Athletico Madrid wanda kungiyar kasar Andalus tayi nasara inda ta doke Nijeriya 3-2.
Bayan ga Congo Nijeriya zata kara buga wasannin sada zumunci da kasar Czech Republic da Ingila a ranar 2 da 6 ga watan Yuni kafin ta garzaya Rasha domin damawa a gasar World cup.
Yaya kuke ganin wasan zai tashi yau?