Ali Nuhu: Jarumi ya bayyana cewa bashi da ra'ayin shiga siyasa

Ali Nuhu

Ali Nuhu wanda ke safarar basira da kwarewarsa a masana'antar fina-finan turanci ya bayyana cewa zai rungume aikin idan ya samu damar fitowa a fina-finan masana'antar Hollywood ta kasar Amurka.

Jarumi mai tauraro kuma jigo a masana'antar fim ta Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana cewa shi da harkar siyasa sun kafar wando.

Duk da farin jini da daukaka da ya samu, Sarkin kannywood ya bayyana cewa ba zai bi sahun wasu daga cikin abokan sana'ar shi.

"Ba ni da ra'ayin siyasa ko kadan, ni fim ne sana'ata ba siyasa ba." ya bayyana yayin da ya zanta da wakilin BBC.

 

Ali Nuhu wanda ke safarar basira da kwarewarsa a masana'antar fina-finan turanci ya bayyana cewa zai rungume aikin idan ya samu damar fitowa a fina-finan masana'antar Hollywood ta kasar Amurka.

Yana mai cewa "Ni duk fim din da ya biyo ta hanyata in dai an min tayinsa to zan shiga, in dai har ina jin harshen da za a yi fim din da shi,".

Yayi karin bayani ga masu korafi cewa baya fitowa a fina-finan kudancin kasar kamar yadda ya saba a da.

"Ga masu cewa ba sa ganina a baya-bayan nan a fina-finan Kudancin Najeriya, to sai dai idan ba sa kallon sabbin fina-finai ne don ba a dade ba ma na yi wani fim mai suna "Banana Island." yace.

 

Daga karshe tauraron fina-finan hausa ya bayyana cewa aikin shi bata hana shi kula da iyalin shi duk da zirga-zirgar da harkar fim ta kunsa. Ya bayyana cewa yana samun lokaci sosai wajen kula da iyalensa musamman ma a cikin wata mai alfarma da ake ciki yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post