Abu kamar a fim: Wani matashi ya hau bene ba tare da fargaba domin ceto rayuwar jariri

matashi ya ceci rayuwar jariri

Dan kasar mali wanda ya koma Faransa ya nuna bajinta wajen ceton rayuwar wata jaririya da ta makale a bene mai dogon tsawo

Wani bakin haure a kasar Faransa mai suna Mamoudou Gassama ya nuna kwazo wajen ceton raywar wata jaririya da ta makale a wata gidan sama.

Lamarin ya faru ne a yankin Northern Paris na babban birinin kasar a ranar asabar 26 ga watan Mayu.

 

Dan asalin kasar Mali ya nuna bajinta wajen yin haka inda ya hau benaye da dama kafin ya kai ga inda jaririyar take.

jama'a da dama sun yaba masa bisa kokarin da yayi wajen yin nasarar kubutar da jaririyar.

Mamoudou Gasama wanda ke da shekaru 22, ya bayyana cewa yayin da yake yunkurin ceto rayuwar ta, bai yi la'akari ko tunanin rayuwar sa.

Kamar yadda ya shaida ma yan jarida gabanin lamarin, matashin yace sai bayan ga ya ceci rayuwar diyar yayi ta kyarma.

Bisa bajinta da ya nuna, shugaban garin Paris tayi masa kira ta musamman domin mika godiyan ta tare da yi masa kyakkyawar albishir.

Bugu da kari matsahin ya hadu da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron inda shugaban ya mika masa takardar zama dan kasa tare da bashi aiki a hukumar agaji dake kashe gobara ta kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post