Boko Haram: Maboyar yan ta'ada zai koma wurin yawon bude ido

Buratai says Boko Haram has been completely defeated

Babban Hafsan sojin Najeriya, Laftanar janar Tukur Buratai ya bayyana aniyar  yin haka

Rundunar sojojin Nijeriya ta sanar cewa, maboyar kungiyar boko haram wato dajin sambisa zai koma wurin yawon bude ido.

Babban Hafsan sojin Najeriya, Laftanar janar Tukur Buratai ya bayyana aniyar  yin haka a wata sako da mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai ya wallafa a shafin sa na twitter.

Ya ce sojoji za su hada gwiwa da hukumar kula da wuraren yawon bude ido ta kasa domin ta taimaka wajan farfado da kimar dajin, domin masu yawon bude ido daga kasashen waje su samu damar ganin namun daji.

Wannan matakin ya biyo bayan ikirarin da sojojin suke yi na cewa sun kori yan ta'adar daga dajin

Kafin mayakan boko haram sun mayar da dajin mafakar su, dajin sambisa ya kasance wurin yawon shakatawa a tun zamanin mulkin mallaka na turawa.

Kamar yadda tarihi na nuna, a wancan lokacin akwai namun daji irin su Zaki da Giwa da Kura da tsuntsaye da kuma gidajen laka da aka gina musamman domin masu yawon bude ido.

Sai dai rashin kula ya sa dabbobin da ke dajin mutuwa kuma gidajen lakan da hanyoyin da ake bi suka lalace, kuma babu ruwan sha da wutar lantarki.

Post a Comment

Previous Post Next Post