Yasuf Buhari: Dan shugaban kasa ya samu sauki ya dawo gida

Yusuf Buhari ya samu sauki ya dawo gida

Yayin saukar sa daga jirgin sama ya samu tarba daga karamin ministan kiwon lafiya da sauran yan uwan sa.

Babban dan shugaban kasa Yusuf Buhari ya samu sauki sakamakon raunukan da ya samu sanadiyar hatsarin babur da ya rutsa dashi watan Disamba na bara.

Bayan jinyar da yaje yi a kasar jamus matashin ya dawo kasar Nijeriya jiya laraba 28 ga watan Febreru.

Yayin saukar sa daga jirgin sama ya samu tarba daga karamin ministan kiwon lafiya da sauran yan uwan sa.

Kai tsaye bayan saukar sa, Yusuf ya garwaya fadar shugaban kasa inda ya gaisa da mahaifin sa shugaba Muhammadu Buhari.

*Zahra Buhari tayi karin haske game da hatsarin dan uwanta

Tun cikin watan karshe na bara aka tafi dashi kasar jamus domin jinya bayan kwatar dashi da aka yi a wata asibiti dake nan garin Abuja.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa a fannin yadda labarai Garba Shehu ya fitar, Yusuf ya samu karaya sanadiyar hatsarin da ya rutsa dashi yayin da yake tsere da babur a daren ranar 26 ga watan disamba na 2017.

Post a Comment

Previous Post Next Post