Atiku yace inda shine shugaban kasa da ya mayar da yan sanda dake tsaron masu hannu da shuni na kasar zuwa makarantu dake arewa maso gabbas domin kare yaran makaranta
Tsohon mtaimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya soko gwamnatin shugaba Buhari kan sakacin da ta wanda ya kai ga sace yan matan makarantar Dapchi su 110 da boko haram tayi.
Tsohon jigon jam'iyar APC wanda ya sauka sheka zuwa asalin jam'iyar da ya samu matsayin mataimakin shugaban kasa a cikin ta wato PDP yace jam'iya mai ci ta gaza bayar da kariya ga yaran.
Yayi wannan tsoacin ne yayin da ya zanta da jaridar Thisday.
Atiku ya bayyana irin tsokacin ta baci da jam'iyar APC tayi ga mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sanda yan ta'adar boko haram suka sace yan matan chibok.
*Iyayen yan matan da aka sace sun kai koken su farfajiyar majalisar tarayya
Kai ga yanzu Atiku ya soki gwamntin APC wanda ta gaza koyi darasi bayan satar yan matan chibok da aka sace cikin watan afrilu na 2014.
Alhaji Atiku yace inda shine shugaban kasa da ya mayar da yan sanda su 150,000 dake tsaron masu hannu da shuni na kasar zuwa makarantu dake arewa maso gabbas domin kare yaran makaranta.
A wata bayanin da tsohon sufeton yan sanda Mike Okiro yayi, tsohon jigon hukumar yan sanda yace jami'an hukuma 150,000 ke tsaron masu hannu da shuni na kasa.
Da wannan dalilin Atiku yake Allah wadai da sakacin gwamnatin tarayya wajen tabbatar da tsaron da dinbim yara dake makaranta.
Yayi kira ga gwamnati da ta dauki mataki wajen ganin yiuwar haka bata faru ba a kasar.