
Shugaban zai halarci bikin tare da ministan ayyukan waje Geoffrey Onyeama da mashawarcin shi a kan harkar tsaro Babagana Monguno
Ana sa ran cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yadda zango zuwa kasar Ghana domin halartar bikin shekara 61 da samun yancin kai.
Kakakin shugaban Femi Adeshina ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar lahadi a garin Abuja.
A bisa sanarwar shugaba Buhari shine bako na musamman wanda kasar Ghana ta gayyata zuwa bikin wanda zai gudana a filin Independence square dake Accra ranar talata.
Kakakin yace shugaban zai yi amfanin da wannan damar wajen kara kulla kyakkyawar alaka tsakanin gwamnatin da jama'ar kasashen Nijeriya da Ghana.
A bisa sanarwar shugaban zai samu rakiya daga ministan ayyukan waje Geoffrey Onyeama da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Babagana Monguno.
Shugaban zai dawo kasar ranar talata bayan kammala bikin.
Tags:
News