Shugaban kasa: Buhari ya daga kofin duniya a fadar sa

That moment when the FIFA World Cup Trophy was lifted by President Buhari

Kofin ya sauka a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja cikin jirgin kamfanin Coca-Coca a daidai karfe 11 na safe

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya daga kofin kwallo kafa na duniya yayin da tawagar hukumar kwallon kafa na FIFA ta gabatar masa da kofin a fadar sa dake Villa.

Wannan yana daga cikin shirye-shiryen da hukumar keyi na zagaya birane da kofin kafin fara gasar cin kofi wanda zai gudana cikin watan Yuni.

Cikin shirin da FIFA ke yi kafin gasar bana, kofin zai zagaya birane 91 dake kasashe 51 na duniya.

Kofin dai ya isa kasar Nijeriya ranar laraba da misalin karfe 11 na safe cikin jirgin kamfanin Coca cola mai dauke da yan rakiya cikin su harda tsohon dan wasan Faranasa Christian Karembeu.

 

Kofin dai ya samu tarba daga ministan wassani Solomon Dalung da shugaban hukumar kwallo na Nijeriya Amaju Pinnick da sauran masu hanu da shuni na hukumar.

Wannan shine karo na uku da kofin alfahari ke shiga kasar Nijeriya cikin karo hudu da rangadin zagayawa da kofin a kasashen duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post