Sarkin Kano na bogi: An kama matashi dan shekara 20 mai yaudarar jama'a da sunan sarkin Kano a  Instagram

An kama matashi dan shekara 20 mai yaudarar jama'a da sunan sarkin Kano a  Instagram

Matashin mai shekaru 20 ya shiga hannu ne bisa laifin yaudarar mutane wai shine sarkin kano mai martaba Muhammad Sanusi na biyu a dandalin Instagram.

Jami'an yan sandan jihar Kano sun kama wani matashi mai fakewa wajen yaudarar jama'a a kafara sada zumunta na instagram.

Matashin mai shekaru 20 ya shiga hannu ne bisa laifin yaudarar mutane wai shine sarkin kano mai martaba Muhammad Sanusi na biyu a dandalin Instagram.

Shafin wanda matashin ya kirkira ta samu alamar tabbatarwa daga kamfani kuma da wannan alamar yake jawo jama'a zuwa shafin domin mafi yawanci ana sa ran cewa tabbas Sarkin ne.

Yan sanda sun kama shi bayan watannin da neman shi kuma kamar yadda suka sanar ana gudanar da bincike kan ayyukan da aiwatar ta hanyar shafin. Sun kara da cewa matashin yana bada haddin kai wajen bada bayanai kan binciken da suke kan laifin.

Tun kwanakin baya dai shi Mai martabar sarkin kano ya sanar cewa baya kawance a shafukan sada zumunta don haka jama'a su kiyaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post