Kamar yadda ya sanar wannan yana daya daga cikin buri da yake neman cinma cikin shekarar 2018.
Sananne mai shirya fim kuma jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi yayi sabuwar mota kirar Mercedes benz
Jarumin ya sanar da haka a shafin sa na Instagram tare da hoton motar don nuna farin ciki da yi ubangiji godiya.
Kamar yadda ya sanar wannan yana daya daga cikin buri da yake neman cinma cikin shekarar 2018.
Suma dai sauran abokan sana'ar shi da masoyan shi masu bibiyar shafin sa na kafar sada zumunta sun taya shi murna.
Nuhu Abdullahi yana daya daga cikin jarumai matasa da tauraruwar su ke haskawa a masana'antar Kannywood. Ya fara da shirya fina-finai kana ya sauya wajen fitowa a cikin su.
Jarumin wanda ya shiga masana'antar cikin 2009 yayi kaurin suna bayan fitowar shi cikin shirin "kanin miji" kuma har yanzu ana jin duriar sa.
Tags:
News