
An biya sadakin N50,000 auren Idris Ajimobi da Fatima Ganduje wanda aka daura a masallacin fadar sarkin Kano ranar asabar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari shine wakilin ango yayin da Bola Tinubu ya zamanto waliyi auren dan gwamnan jihar Oyo da diyar Gwamnan Kano.
An daura auren Idris Ajimobi da Fatima ganduje a msallacin dake fadar sarkin Kano ranar asabar 3 ga watan maris 2018.
*Kalli kayan lefen da aka kai wa diyar gwamnan jihar Kano
Shugaban kasa ya biya sadakin N50,000 a madadin ango ga jigon APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas wanda ya zamanto waliyin amarya.
Gwamnoni 22 da suka halarci daurin auren tare da manya manya masu ruwa da tsaki a harkoki daban daban.
Sauran baki da suka halarci daurin auren sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Sarkin Kano mai martaba Alhaji Muhammad Sanusi na biyu, Aliko Dangote, Abdulsamad Isiaka Rabiu, ministoci da sauran su.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya aurar da diyar shi ga dan gwamna Abiola Ajimobi wanda haduwar su ya nuna a yiwuwar aure tsakani kabilu daban daban kasancewa shi angon bayarabe ne kuma ita amaryar bahaushiya ce.
Anyi bukuwa da dama na shagalin auren su na kusan mako daya. Jim kadan bayan daura auren su angon ya yadda zango da amrayar shi zuwa kasar waje inda zasu yi hutun amarya da ango.