Dandazon jama'a suka fito domin yima shugaban maraba yayin da yake zagayawa a garin Jos babban birnin jihar.
Shugaban kasa ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Filato.
Jiya alhamis 8 ga watan Maris shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Filato.
Shugaban ya sauka filin jirgi na garin Jos domin kaddamar da ayyukan cigaba da gwamnatin jihar ta aiwatar.
Gwamnan jihar Simon Lalung da tawagara ma'aikaan jihar sun tarbi shugaban yayin da ya sauka daga jirgi.
Dandazon jama'a suka fito domin yima shugaban maraba yayin da yake zagayawa a garin Jos babban birnin jihar.
Shugaba Buhari ya gana da sarakunan gargajiya na jihar karkashin jagorancin Bon gwon Jos Mai martaba Jacob Gyang Buba inda suka tattaunawa kan matsalolin tsaro da hanyar kawo karshen barkewar rikici a jihar.
Tags:
News