Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya ziyarci jihar Taraba

Isowar shugaba Buhari jihar Taraba

Shugaban ya gana da sarakunan gargajiya da manoma da makiyaya kan rikice-rikice dake faruwa tsakaninsu a jihar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Taraba domin kai ziyarar jajantawa ga al'ummar da rikici ya shafa.

Shugaban ya isa Jalingo jiya litinin 5 ga wata inda ya samu tarba daga gwamnan jihar Darius Ishaku da mukarraben sa.

Jim kadan bayan saukar sa shugaban ya gana da manoma da makiyaya domin tattaunanwa kan hanyar dakile rikice-rikice dake faruwa tsakaninsu a jihar.

Shugaban zai zarce zuwa jihar Yobe, Benue, Zamfara da Rivers.

Shugaban ya dauki matakin ziyartar jihohin da rikici ya shafa domin jajanta masu bayan rahotannin da ya samu daga jami'an tsaro kan lamarin.

 

Jama'a da dama sun soki shugaban bisa daukar wannan matakin bayan kwanaki da dama da faruwar rikice-rikicen.

Ana zargin shugaban da nuna halin ihu bayan harbi kan jajanta ma jama'a da rikicin ya shafa. Mafi yawanci dai wannan soki yana faruwa ne a kafafen sada zumunta.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post