Taron wanda aka gudanarwa a garin Epe dake jihar Legas ya samu halartar manya masu ruwa da tsaki a fannoni daban daban na kasar harda yan kasar waje
Manyan jagorori da masu ruwa da tsaki a fannoni daban daban sun halarci taron wayar dakai da yin muhawara kan tattalin arziki da zuba jari da gamayyar gwamnatin Kano da Legas suka shirya.
Taron wanda ya aka kaddamar jiya laraba 28 ga watan febreru garin Epe dake nan jihar Legas ya samu halartar manyan fuskokin masu ruwa da tsaki a fannoni daban daban.
Taron wanda muhawara wanda zai gudana cikin kwana biyu ya samu kaddamarwa daga mataimakin shugaban kasa Ferfesa Yemi Osinbajo.
Gwamnonin jihar Kano da Legas wadanda suka shirya taron sun hakarci taron tare da takwaran su na jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu.
Banda gwamnoni su da mataimakan su suma yan majalisar tarayya na sama da na kasa da kuma na jihohin guda biyu sun halarci taron
Suma sarakunan gargajiya sun halarci zauren taron inda sarkin Kano mai martaba Muhammad Sanusi na biyu ya bada jawabi ta musamman kan fa'idar gudanar da ire-iren taron don samad da cigaba a fannin kasuwanci. Hakazalika shima sarkin Legas Oba Rilwan Akiolu ya garzaya farfajiyar tare da sarkin garin Epe inda taron ke gudana.
A jawabin sa Mai martaba sarkin Kano ya sanar cewa ire-iren wannan matakin da jihohin suka dauka na kula alaka da juna kan harkar kasuwanci zai taimaka matuka wajen mayar da arkalar arzikin kasa sauyawa daga man fetur zuwa harkar kasuwanci.
A bangaren yan kasuwa kuwa attajirin da kasuwa mafi kudi a afrika Alhaji Aliko Dangote tare da shugaban kamfanin BUA Alhaji Abdulsamad Isiaka Rabiu da shugaban kamfanin Folawiyo groups Yinka Folawiyo ba baro su baya ba.
Suma yan kasuwa a bangarori daban daban na cikin kasar har ma da yan kasar waje da kuma kwararrun masana zasu bada jawabi a karon wanda za'a kammala ranar alhamis 1 ga watan Maris.
Manufar taron dai zai taimaka wajen kulla kyakkyawar tsakanin jihohin wadanda suka kasance cibiyoyin kasuwani wanda ake takama dasu a kasa. Zai kara taimaka wajen jawo masu zuba jari wajen bunkasa harkar kasuwanci tare da sammad da ayyukan yi ga al'umma.
Kalli sauran hotunan nan kasa