Gwamnan yace malamai sun tsallake jarabawan da aka shiryawa masu ta barauniyar hanya amma basu samu nasarar samun aiki sakamakon gwajin da aka yi masu na rubuta wasika amincewa da fara aikin koyarwa
Gwamna jihar kaduna Malam Nasir El-rufai ya bayyana cewa wasu daga cikin sabbin malamai da gwamnatin sa ke kokarin dauka aiki sun nemi barauniyar hanyar yayin tantance su.
Gwamna yayi wannan ikirarin a wata muhadara da wata cibiyar cigaban al'umma ta hada a garin Abuja ranar alhamis 8 ga wata.
*Duk malamin da ya tafi yajin aiki, ya sani cewa iya bakin aikin sa kenan
Gwamnan yace malamai sun tsallake jarabawan da aka shiryawa masu ta barauniyar hanya amma basu samu nasarar samun aiki sakamakon gwajin da aka yi masu na rubuta wasika amincewa da fara aikin koyarwa Sabbin malamai sun gaza rubuta wasika amincewa da aiki bayan an sanar dasu cewa sun samu aikin.
Kan wannan hukumar gwamnatin dake tantance su ta yi masu sallama.
Gwamna dai ya sha alwashi samad da ingantacciyar cibiyoyin koyar da ilimi a jihar tare da kwarerun malamai don bayar da ilimi managarta ga al'ummar jihar.