An cafke barawon mai suna Micheal wanda dan aji hudu ne a jami'ar yayin da yake kokarin yin sata a dakin wasu a makon da ya gabata.
Wani dalibin jami'ar Bayero dake Kano ya gamu da fushin dalibai inda suka garkame shi yana satar masu kaya.
An cafke barawon mai suna Micheal wanda dan aji hudu ne a jami'ar yayin da yake kokarin yin sata a dakin wasu a makon da ya gabata.
kamar yadda rahotanni ta fito, tun ba yau ba ake zargin shi da aikata mumunar aiki ga yan uwanshi dalibai. Dubun shi ya cika bayan ya nemi ya shiga wani dakin domin yin sata inda dalibai suka kama shi har suka yi mai bugun jina-jina.
Dai taimakon jami'an tsaro barawon ya kubuta daga hannun wadanda suka kama shi.
Tags:
News