Biki Bidiri: Jaruma Sadiya Adam zata amaryace, kalli hotunan kafin auren ta

Sadiya Adam da angonta

Jarumar kannywood tana shirin shiga dakin aure, za'a daura aurenta ranar lahadi 1 ga wata afrilu

Jarumar masana'antar fim ta Kannywood mai tauraro Sadiya Adam tana shirin shiga sahun gaba, zata shiga dakin aure.

Za'a daura auren ta da angon ta Alhaji Sanusi Ahmad ranar lahadi 1 ga watan Afrilu na 2018 a masallacin Umar bin khattab dake Zaria.

Hotunan kafin auren ta yana ta yawo a shafuka da dama na yanar gizo inda jama'a suna ta mata murna.

 

Abokan aikin ta na masana'antar kannywood sun yi mata farin ciki inda  suka wallafa hotunan kafin auren ta a shafukan su a kafar sada zumunta tare da yi mata fatan alheri.

Muna masu fatan alhari, Allah ya bada zaman lafiya, Ameen.

Post a Comment

Previous Post Next Post