Tsohon gwamnan jihar Alhaji Aliyu Akwe Doma ya rasu yana da shekaru 78 a duniya
Jihar Nasarawa tayi babban rashi mutuwar tsohon gwamnan jihar Alhaji Aliyu Akwe Doma.
Ya rasu ne a wata asabiti dake kasar isiraila sanadiyar rashin lafiya da yake fama da ita tun ba yau ba.
Daya daga cikin yan uwan marigayin ya sanar da mutuwar shi.
Marigayin shine gwamnan jihar Nasarawa daga shekara 2007 zuwa 2011 karkashin jam'iyar PDP.
Ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.
Tags:
News