A jihar filato: Ma'aikatan jihar Filato zasu samu hutun kwana daya kan ziyarar shugaban kasa

Plateau State governor, Simon Lalong

Shugaban zai kai ziyara kaddamar da ayyuka jihar ranar alhamis 8 ga wata

Gwamnatin jihar Filato ta bada hutun kwana daya ga ma'aikatan jihar kan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo jihar.

Ana sa ran isowar shugaban garin Jos ranar alhamis tare da mukarraben sa domin kaddamar da ayyukan cigaba da gwamnatin jihar Filato ta gudanar.

Bisa sanarwa da shugaban ma'aikata na jihar Izam Azi ya fitar, gwamnatin ta dauki wannan matakin domin ma'aikatan jihar suma suyi maraba sa zuwan shugaban.

A cewar shi jama'a da dama zasu fito kwai da kwarkwatar su wajen tarban shugaban kan ziyarar kaddamar da ayyuka da zai kao jihar ranar Alhamis 8 ga wata.

Kwamishnan labarai na jihar Datti Yakubu ya kara da cewa za'a hana tafiya wasu wurare ga jama'a musamman a wuraren da shugaban zai kaddamar da ayyuka.

Post a Comment

Previous Post Next Post