
Wannan labari ya biyo bayan wasu shafuka na yanar gizo suna ta wallafa cewa Yusuf ya rasu a yammacin ranar talata 20 ga wata.
Fadar shugaban kasa ta karayata jita-jita dake yaduwa a kafafaen sada zumunta na cewa dan shugaban kasa Yusuf Buhari ya mutu.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkar watsa labarai kan shafukan sada zumunta na zamani Malam Bashir Ahmad ya sanar da haka yayin da zanta da wakilin BBC.
"Yusuf Buhari yana samun sauki a asibitin da yake jinya a kasar Jamus kuma likitoci suna sake duba kansa da ya bugu da kuma kafarsa."
*Jiga-jigan yan siyasa sun tura ma iyalin shugaban kasa Sakonnin jaje
Wannan labari ya biyo bayan wasu shafuka na yanar gizo suna ta wallafa cewa Yusuf ya rasu a yammacin ranar talata 20 ga wata.
Malam Bashir ya karyata labarin domin bata da kamshin gaskiya a cikin ta inda ya kara da cewa "ko jiya [Talata] na yi magana da 'yar uwarsa da ke jinyarsa a asibitin Jamus kuma ta shaida min cewa yana samun sauki sosai."
Hatsarin Babur
Bayan jinyar da yayi a wata asibitin dake garin Abuja an tafi da Yusuf kasar Jamus inda yake cigaba da jinyar ibtila'in da ya abka mai sanadiyar hatsarin babur da ya samu.
A safiyar ranar laraba 27 ga wata kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar cewa Yusuf Buhari ya ji rauni tare da karaya sanadiyar hatsarin babur da ya samu a yankin Gwarinpa nan babban birnin tarayya daren ranar 26 ga watan yau.