Femi Adeshina yana mai cewa har yanzu ba'a gama yakar boko haram ba amma an rage karfin su kuma nan bada jimawa ba za'a samu nasara a kan su
Babba mai baiwa shugaban kasa shawara kan kannun watsa labarai Femi Adeshina ya bayyana cewa fadar shugabanm kasa ta amince da acewa bata samu cikakkiyar nasara kan mayakan boko haram kamar yadda a zato.
Yace duk da cewa har yanzu ba'a gama gwaggwarmaya da yan ta'addar ba amma ana dap da samun hakan.
"indai mai yakar su gaba dayan su toh lalle bamu samu nasara ba amma maganar rage karfin su, lalle mun ci nasara a wannan bangaren"Yace.
kakakin ya bayyana hakan yayin da ya zanta da gidan telibijin na channels a cikin shirin tattaunawa a kan harkar siyasa ranar 25 ga wata.
Duk da hare-hare da yan boko haram suka kai wanda keyi ma harkar tsaro barazana tare da sabon farmaki da suka kai garin Dapchi wanda suka yi awon gaba da yan matan makaranta su 105, kakakin yace gwamnatin shugaba Buhari ta samu cigaba wajen yakar ta'adanci a kasar fiye da yanda suke a gwamnatocin da.