Shugaban kasa: Zan yi iya bakin kokari na wajen kubitar da duk dan kasa dake garkame a hannun Boko Haram

Shugaban kasa ya hadu da malaman jami'ar Maiduguri da yan ta'ada suka sace

Shugaban yayi wannan alkawarin yayin da amshi bakoncin malaman jami'ar Maiduguri da yan ta'adar suka saki kwanan baya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin duk wani mataki da zai taimaka wajen ceto duk wani da yan ta'addar boko haram suka garkame daga hannun su.

Shugaban yayi wannan alkawarin yayin da ya amshi bakoncin malaman jami'ar Maiduguri da yan ta'addar suka saki kwannan baya a fadar sa dake nan Villa.

Malaman suna cikin tawagar masana wajen gano danyen mai a yankin tafkin Chad dake nan jihar Borno.

Tare da malamai, shugaban ya gana da mata 10 da yan ta'addar suka yi awon gaba dasu.

Malaman da matan sun fito daga zauren yan ta'adar ranar 10 ga watan Febreru 2018 bayan yarjeniyar da ya faru tsakanin yan ta'addar da gwamnatin tarayya.

 

"Farin cikin dake tattare dani baya iya misaltuwa ganinwadanda yan ta'adar boko haram suka sace. Zamu dauki duk wani mataki da ya kamata wajen ganin cewa mun kubitar da duk wani dan kasar dake hannun yan ta'adar. Rayuwar  ko wani dan kasa yana da muhimmanci. Shugaban ya sanar.

Ya nun farin cikin sa ganin cewa malaman da matan sun koma ga iyalin su tare da yin kira da sauran yan kasar da su taya su murna.

Post a Comment

Previous Post Next Post