Shugaban kasa: Sace yan matan makaranta bala'i ne wanda ya shafi kasa baki daya

Shugaban kasa ya baiwa hukumar hana zamba damar tuhumar Babachir da Oke

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ta hannun babban mai taimaka ma sa a kan sha’anin yada labarai, Malam Garba Shehu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari  yana ba da hakuri kan  harin da ya yi sanadiyyar bacewar dalibai ‘yan mata a Makarantar Sandaren Kimiyya da Kere-kere da ke garin Dapchi a Jihar Yobe. Shugaban ya bayyana abin da ya faru a matsayin bala’i da ya shafi kasa baki daya ba wani yanki guda daya ba.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ta hannun babban mai taimaka ma sa a kan sha’anin yada labarai, Malam Garba Shehu.

Ya yi bayanin cewa yana jin zafi da radadi irin wanda iyayen yaran da suka bace suke ji kuma ba zai sarara ba har sai ya tabbatar da cewa an kubutar da ‘yan matan. Ya ce gwamnatin tarayya za ta tura karin dakaru da jiragen sintiri da za su yi aiki dare da rana a yankin.

“Wannan bala’i ne da ya shafi kasa. Muna ba da hakurin faruwar lamarin kuma muna jin radadin abin. Muna da kyakkyawan fatan cewa jaruman dakarun tsaronmu za su gano inda iyalanku suke tare da dawo da su gida cikin koshin lafiya.

“Gwamnatinmu za ta tura karin jami’an tsaro da jirgin sintiri domin sanya ido a daukacin yankin dare da rana domin ganin an gano daukacin ‘yan matan da suka bacen”.

“A lokacin da na samu labarin harin da aka kai makarantar da kuma bayanin cewa shugabanni a yankin ba su gano inda daliban suke ba, nan take na tura wata tawaga mai karfin gaske domin binciko asalin abin da ya faru.

“Na kuma umurci hukumomin tsaro su tura isassun dakaru tare da amfani da dukkan karfinsu wajen tabbatar da cewa yaran sun dawo cikin koshin lafiya da kuma cafke wadanda suka kawo harin a gurfanar da su a gaban kuliya”. Sanarwar ta kara da cewa, al’ummar kasar nan baki daya suna tare da iyalan ‘yan matan, da gwamnati da sauran jama’ar Jihar Yobe, ba za a bar su su kadai ba da juyayin abin,, in ji sanarwar.

A yammacin ranar litinin 19 ga wata yan ta'adda daake sa ran cewa yan boko haram ne suka kai hari garin Dapchi inda ma har suka yi awon gaba da yan matan makarantar su 94.

Shugaban ya tura wasu ministocin shi garin domin tantance asali yadda harin ya faru tare da jajanta ma al'ummar jihar Yobe.

A bayanin shi bayan ziyarar da ya kai makarantar yan matan da aka sace, ministan watsa labarai Lai Muhammed ya bayyana cewa yan ta'addar na neman watsa ma gwamnatin shugaba Buhari kasa a ido amma gwamnati zata samu rinjaye a kan su bisa ga kokarin da jami'an tsaro keyi wajen kawo tarshen ta'adancin su.

A cewar yan ta'addar boko haram na magagin kunya bayan nasarar da sojojin suka samu na korar su daga gidauniyar su dake dajin sambisa.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post